Property damage
| Bayanai | |
|---|---|
| Ƙaramin ɓangare na | damage (en) |
| Has cause (en) | property damage (en) |

Lalacewar dukiya (wanda a wasu lokuta ake kira lalata dukiya) na nufin lalacewa ko rushewar dukiyar da ba za a iya motsa ta ba ko dukiyar mutum mai zahiri, wanda sakaci, lalata da gangan, ko kuma wani al’amari na dabi’a ya haifar.
Rushewar dukiya (wanda a wasu lokuta ake kira lalata dukiya, ko kuma lalata dukiya ta laifi a Ingila da Wales) wani ɓangare ne na lalacewar dukiya wanda ya ƙunshi lalata dukiya sakamakon aikata laifi da gangan, kuma doka na hukunta shi a matsayin laifi..[1][2][3] Rushewar dukiya ya ƙunshi vandalism (lalata, rushewa, ko ɓata kamannin dukiya da gangan), rushewar gini ta hanyar fashewa (rushe dukiya ta amfani da abubuwan fashewa), da ƙona dukiya da gangan (lalata dukiya ta hanyar wuta), da sauran makamantan laifuffukan da suka ƙunshi yin barna ko rushe dukiya ta mutum ko dukiyar da ba za a iya motsa ta ba ba bisa ƙa’ida ba.
Kotuna na iya ba da umarnin lalata dukiyar da ta saba wa dokokin mallakar ilimi.[4]
Da'awar inshora
[gyara sashe | gyara masomin]Lalacewar dukiya kuma tana nufin asarar dukiyar zahiri a cikin da’awar asarar inshora, da ta shafi gine-ginen zama da na kasuwanci, da kuma motocin haya.[5] A hadurran ababen hawa, yawanci ana iya samun asarar gine-gine, kayayyakin mutum, da motoci, waɗanda duk ake iya kiran su da lalacewar dukiya..[6]
Dubi kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ (Markus D. ed.). Missing or empty
|title=(help) - ↑ "property damage". LII / Legal Information Institute (in Turanci). Retrieved 2025-05-21.
- ↑ Wagon, Tina (2024-04-09). "What is Considered Criminal Damage to Property". Wheldon Law (in Turanci). Retrieved 2025-05-21.
- ↑ (Carlos M. ed.). Missing or empty
|title=(help) - ↑ "Loss of Use as Property Damage". www.irmi.com (in Turanci). 2021-06-04. Retrieved 2025-05-21.
- ↑ "How Is Property Damage Handled in an Auto Accident?". vaughanandvaughan.com (in Turanci). Retrieved 2025-05-21.